1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta kafa dokar hana zirga-zirga

Binta Aliyu Zurmi
March 24, 2020

Sakamakon karuwar cutar corona a fadin duniya, Birtaniya ta ayyana makwanni uku na hana zirga-zirga.

Großbritannien London | Coronavirus | Boris Johnson, Premierminister
Hoto: picture-alliance/empics

Birtaniya ta bi sahun wasu kasashen duniya da suka kafa dokar hana zirga-zirga, har na tsawon makonni uku, a kokarin ganin sun dakile yaduwar annobar coronavirus.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi game da karuwar wadanda cutar take kamawa a duniya.

Da ya ke jawabi ga al'ummar kasar, Firaminista Boris Johnson ya umurci a rufe dukkan shaguna in ban da na kayan abinci da kuma sayar da magunguna.