1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya za ta hukunta masu tada tarzoma

August 5, 2024

Firanministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi gargadi cewa masu bore za su yi nadamar haddasa tarzoma mafi muni cikins shekaru 13 a kasar.

Zanga-zanga a Birtaniya ta rikide zuwa tarzoma
Zanga-zanga a Birtaniya ta rikide zuwa tarzomaHoto: Danny Lawson/PA/dpa/picture alliance

Firanministan Birtaniya, Keir Starmer da ya zargi masu tsattsaurar ra'ayi da haddasa tashin-tashi nar, ya sha alwashin cewa sai an hukunta duk wadanda ke da hannu cikin tada zaune tsaye, kama daga wadanda suka fantsama kan tituna da kuma masu asassata a kafafen yada labarai. Rikidewar zanga-zanagar ya zuwa tarzoma dai na alaka da kashe wasu yara uku a makon da ya gabata.

An ruwaito cewa, masu zanga-zangar kyamar da baki sun farfasa tagogi a wani Otel da ake amfani da shi wajen tsugunnar da masu neman mafaka a Rotherham da kuma South Yorkshire.