1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta soke atisayen sojinta a Kenya

July 23, 2026

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da soke daya daga cikin atisayen sojinta na shekara-shekara da ke gudana a Kenya.

Firaministan Birtaniya Andy Burnham
Firaministan Birtaniya Andy BurnhamHoto: Victoria Jones/Shutterstock/PA ROTA/Avalon/IMAGO

Matakin ya biyo bayan gaza samun lasisin gudanar da atisayen daga gwamnatin kasar ta gabashin Afirka.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce a yanzu ta mayar da atisayen zuwa wata kasa da ba ta bayyana sunanta ba, amma ta jaddada cewa matakin ba zai shafi hadin gwiwar tsaro da ke tsakanin kasashen biyu ba.

Kenya ta bai wa Birtaniya sansanin horas da sojoji tun bayan samun 'yancinta a 1963, sai dai sansanin ya sha fuskantar ce-ce-ku-ce sakamakon wasu manyan laifukan da ake zargin wasu sojojin Birtaniya da aikatawa.