Birtaniya ta yi fatali da batun zama a EU
March 14, 2019Talla
'Yan majalisar dokokin Birtaniya 334 sun nuna adawa yayin da 85 suka yi na'am da yunkurin sake tambayar 'yan kasar ko suna so su ci gaba da zama a cikin EU ko kuma raba gari da wannan gamayya.
Kwanaki 15 ne suka rage Biratniya ta yi sallama da EU a ranar 29 ga watan Maris 2019, amma har yanzu majalisar kasar da ma al'umma na ci gaba da samun sabani a kan hanyoyin ficewa da kuma kan makomar dangantaka tsakanin sassa biyu.
Su dai 'yan majalisar Birtaniya sun ki amincewa da yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da kungiyar Tarayyar Turai don ficewa cikin ruwan sanyi, suna masu nuna adawa da ci gaba da amfani da dokokin kasuwanci na EU.