Yarima Charles na Birtaniya ya kamu da cutar coronavirus
March 25, 2020Talla
Yanzu haka dai yana samun kulawar likitoci wanda rahotanni suka tabbatar da yana cikin koshin lafiya.
Mai magana da yawun fadar Buckingham, ya bayyana cewa mai dakin yarima Charles, Camila ita ma an mata gwajin cutar amma sakamako ya nuna bata dauke da cutar. Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce tuni Yariman ya killace kansa a wani gidansa a yankin Scotland.
Wannan cuta ta coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya na zama babbar barazana inda yanzu alkalumma mutanen da suke dauke da cutar sun haura mutum dubu dari hudu yayin da wadanda suka mutu suka haura mutum dubu goma sha tara.