Tana kasa tana dabo kan yarjejeniyar EU da Birtaniya
October 18, 2019A Birtaniya da hedikwatar tarayyar Turai a Brussels, an nuna alamun gamsuwa da ta kawo karshen kwan-gaba kwan-baya da aka shafe kusan shekaru uku ana yi. Firaministan Birtaniyar Boris Johnson yace "yana da kwarin gwiwa 'yan majalisa za su amince da yarjejeniyar, inda ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai kyau, tare da cewa idan 'yan majalisa daga dukkan jam'iyyu suka yi kallo da idon basira za su gane fa'idar da ke akwai na su bada goyon baya domin aiwatar da ficewar Birtaniya daga EU a ranar 31 ga watan Oktoba domin cikawa jama'a burinsu da alkawuran da yan majalisa suka sha yi domin tabbatar da wannan manufa."
Jean Claude Juncker na taikacin fitar Birtaniya daga EUAna dai iya cewa har yanzu tana kasa tana dabo kan dambarwar ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai EU. Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai kowannensu ya yi sassauci kan matsayinsa kafin daga bisani a cimma yarjejeniya. Sai dai kuma shugaban hukumar tarayyar Turan Jean Claude Juncker ya ce rabuwar ta zama dole, amma ba haka aka so ba inda ya nuna matukar takaici da ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai, kana kuma abu na gaba dai a yanzu shi ne amincewar majalisar dokokin Birtaniya kan kudirin yarjejeniyar. A ranar Asabar ne majalisar za ta yi zama na musamman domin kada kuri'ar amincewa ko kuma akasin haka kan sabuwar yarjejeniyar.
'Yan siyasan Birtaniya na sukar yarjejeniyar EUTuni dai 'yan siyasar Birtaniyar suka fara mayar da martani kan wannan yarjejeniya. Kungiyar Tarayyar Turai ta amince Ireland ta Arewa ta bar hadakar shige da fice ta kwastam yayin da a daya bangaren kuma Birtaniya za ta jure wa dacin barin Ireland ta Arewa yin biyayya ga dokokin Kungiyar Tarayyar Turai da suka shafi cinikayya. Shugabar jam'iyyar DUP ta Ireland ta Arewa Nigel Dudd wadda Boris Johnson ke fatan samun goyon bayansu ta ce ko kusa ba za su bada goyon baya ba.
Haka shi ma a nasa bangaren shugaban babbar Jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya nuna takaici da yarjejeniyar yana mai cewa "Firaminista ya cimma yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai wadda ba ta bamu 'yancin walwala tsakanin mu da Ireland ta Arewa ba, saboda ta samar da binciken kwastam akan kogin Ireland. Sannan abu na biyu bata kawar da damuwar da muka nuna a yarjejeniyar Theresa May ba, saboda haka za mu yi adawa da yarjejeniyar a majalisa a ranar Asabar."
Amincewa da yarjejeniyar dai abu ne da zai farantawa kungiyar tarayyar Turai sabanin ficewa babu yarjejeniya inda bangarorin biyu za tafka babbar hasara, a waje guda kuma idan majalisar dokokin ta amince firaministan Birtaniya zai nuna wa duniya cewa kamar yadda ya yi alkawari babu gudu babu ja da baya zai fidda kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba komai rintsi kuma ta tabbata.