1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a mayar wa Najeriya kayan tarihi

Abdourahamane Hassane
May 11, 2021

Akwai kayayyaki tarinhin daular Benin da suke watse a kasashen duniya da dama, wadanda Turawan mulkin mallaka suka yi awon gaba da su, kuma suka sayar da su.

Köln | Benin Bronzen im Rautenstrauch-Joest-Museum
Hoto: Johan von Mirbach/DW

Lokacin da dakarun 'yan mulkin mallaka nA Birtaniya suka mamaye tsohuwar Daular Benin ta Najeriya a 1897 sun yi awon gaba da dubban kayayyaki kira na gargajiya na tarihi masu daraja wadanda wasun su a yau ake samunsu a cikin gidajan ajiye kayan tarihi na Birtaniya. Misali jamia'ar Abeerden da ke a Birtaniyar tana rike da wani abun rufe fuska dan madundumi ko Facemask da aka sato daga gidan sarkin tsofuwar daular ta Benin  wanda yanzu take son ta mayar da shi.

Wasu a gidajan tarihi na tsofin shugabanin yan mulkin mallakar, wasu a ckin jami'o'i Neil Curtice shi ne daraktan gidan ajiye kayan tarihi na jami'ar Aberdeen.

"An sace kayayyaki an yi wasosso kuma kayayyakin da aka saton bai kamata ba a ce sun zama mallakar jami'ar mu ba.

Kayan tarihin BeninHoto: Daniel Bockwoldt/dpa/picture alliance

Abun rufe fuskar na gidan sarautar ta tsofuwar daular ta Benin, wadanda suka kasance jagororin jami'ar ta Aberdeen sun sayeshi a shekara ta 1957 a wani wantaran da aka yi kudi tsaba Fam 750 wanda a yanzu ake ajiye da shi a gidn addana kayan tarihi na jami'ar ta Aberdeen. Kusan shekara guda ke nan da ake tafka muhawara a game da irin taadin da 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka aikata a nahiyar Afirka na yin fashi a game da kayan tarihin kamar su dan  butuntume, gumaka na zinari  da azurfa da sauran kadarori.

Dan Hicks ma'aji a gidan ajiye kayan tarihi na Pitt Museum da ke a Oxford ya ce dira mkiya da da sojojin mulkin mallakar suka yi a 1897 a Benin sun wasashi abubuwa da dama.

''Tabbas an bi didigi tun daga farko har karshe na kayayyakin da ake da su a lokacin a masarautar kafin suka yi awon gaba da su. An yi musu kwace na addini da 'yanci da kuma al'adu

Bayan jami'ar Aberdeen akwai wasu jami'oi Birtaniyar da suka sanar da sake mayar a kayyayakin na tarihi da  Turawan mulkin mallaka na Birtaniya sukasato. Misali Cocin Anglikan tana son sake mayar da wasu butuntumi guda biyu na tagulla wadanda ta samesu shekau 40 da suka wuce.

Yayin da wani kamfannin sayar da kayayyakin wantare ya janye irin kayyakin tarihin da aka sato daga Benin  daga cikin kayan da yakan sayarwa, Hicks ya kara da cewar.

Kayan tarihin Benin da ke JamusHoto: Johan von Mirbach/DW

"Yadda muka yi aka sake dawo da kayyaykin da yan mlkin Nazi suka wasashe ya kamata mu yi haka a game a irin sace-sace da aka yi a tsofuwar daulr Benin ta can dauri".

Alkaluma  sun nuna cewar gidan ajiye kayan tarihi na British Museum ya fi kowanne daga cikinsu yawan kayayyyakin da aka sato daga tsofuwar Daular Benin da ke kudancin tarayyar Najeriya wanda aka kirga kayayyaki daya-daya har 928 wanda ta intanet ma ake iya  ganinsu.

Sai dai ya zuwa yanzu babu alamun gidan ajiye kayan tarihin na Birtaniya ko yana da niyyar sake mayar a kayayyakin tarihin duk da ma cewar ya amince da cear na sata ne.