Shekara daya da soma wa'adi na biyu na mulkin Buhari
May 29, 2020
A Najeriya gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika shekara daya da soma wa'adin mulki na biyu wanda ya hade da zamanin annobar Covid-19 wacce ta yi wa kasar illa a fannoni da dama da suka hada da na lafiya da kuma tattalin arziki.
Batun tsaro da tattalin arziki da ma yaki da cin hanci dai ba su sauya ba a zuciyar 'yan mulkin da ke neman kawo sauyi a cikin Tarrayar Najeriya na lokaci mai nisa. To sai dai kuma ra'ayi tsakanin al'umma ta kasar na banbanta bisa irin sauyin da kasar ta gani bayan share tsawon shekara guda cikin hudu na wa'adi na biyu na mulki na masu tsintsiyar Tarrayar Najeriya.
Duk da annobar Corona da ta sauya daukacin tsari na rayuwar al'umma a duniya dai, babbar nasara a zuciyar 'yan mulkin Tarrayar Najeriyar bayan share shekara guda na zaman ci da kai da ke zaman sabon kwazo cikin kasar a cewar Malam Garba Shehu kakaki na gwamnatin ta Abuja.
Ta dai yi baki ga batun tsaron sakamakon karuwar kisan da ke ta'azzara a sashen Arewa maso Yamma na shugaban kasar, ko bayan batu na tattalin arziki da covid 19 ta lamushe, haka shi kansa batun korar fatara daga iyakokin Tarayar Najeriyar dai na neman komawa ya zuwa mafarkin 'yan mulki a fadar masu adawar kasar da ke fadin gwamnatin kasar ta kasa ta ko'ina.
Coronar cuta ko ko Corona kasuwa dai al'umma ta kasar na shirin share shekaru uku masu zuwa a cikin jagoranci na masu tsintsiyar.
Kuma a fadar kakakin shugaban kasar har yanzu akwai fatan cika daukacin alkawuran da ke tsakanin shugaban kasar da al'ummar ta bayan samun bashin da kasar ke fatan zai kai ta ga aiwatar da daukacin ayyukan da ke gaba.
Mataki na gaba na rayuwa bayan annobar ta Corona dai daga dukkan alamu na zaman mara tabbas ga 'yan kasar da baya ke tunanin sake gina ababe na more rayuwa da nufin ingantar lamura.