1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin wasannin motsa jiki na karshen mako

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim ZMA
April 13, 2026

Arsenal ta yi halin na ta bayan barar da dama a gida da za ta jaddada matsayinta na neman lashe gasar firimiyar Ingila.

Champions League 2025/26 | Viertelfinale | Sporting CP vs. Arsenal | Kai Havertz erzielt das 1:0
Hoto: Armando Franca/AP Photo/picture alliance

-Makamancin hakan ne ya faru ga Borussia Dortmund a kokarinta na taka wa Bayern Munich birkin kaka-gida da ta yi a gasar Bundesligar Jamus tamkar kayan gado.

-Jannick Sinner ya dare kan saman jadawalin kwallon tenis a duniya a matsayin lamba daya, bayan hankado Carlos Alcaraz ta hanyar lallasa shi a wasan karshe na Monte Carlo Masters.

-Muna tafe da sharhi kan yadda zargi ya yi yawa ga hukumar shirya gasar firimiyar Najeriya wajen gaza samar da alkalan wasa nagartattu.

-Har ma da yadda ta kaya a zagayen dab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka.

Bundesliga:

Juma'a

Augburg-Hoffenheim 2-2

Asabar

Borussia Dortmund-Bayer Leverkusen 0-1

RB Leipzig- Borussia Munchengladbach 1-0

Wolfsburg-Eintracht Frankfurt 1-2

Heidenheim-Union Berlin 3-1

St.Pauli-bayern Munich 0-5

Lahadi

Cologne-Werder Bremen 3-1

Stuttgart-Hamburg 4-1

Mainz-Freiburg 0-1

Jadawalin Bundesliga bayan makonni 29

1. Bayern Munich 76        

2. Borussia Dortmund 64            

3. Stuttgart 56        

‘Yan wasa da suka fi jefa kwallaye a gasar

1. Harry Kane - 31 (Bayern Munich)

2. Deniz Undav 18 (Stuttgart)

3. Luiz Diaz Diaz 15 (Bayern Munich)

4. Serhou Guirassy 13 (Borussia Dortmund)

Firimiyar Ingila:

Juma'a

West Ham United- Wolverhampton 4-0

Asabar

Arsenal - Bournemouth 1-2

Brentford - Everton 2-2

Burnley - Brighton & Hove Albion 0-2

Liverpool - Fulham 2-0

Lahadi

Chelsea-Manchester City 0-3

Sunderland-Tottenham Hotspur 1-0

Crystal Palace-Newcastle United 2-1

Nottingham Forest-Aston Villa 1-1

Wasan daren Litinin

Manchester United-Leeds United

Jadawalin Firimiya bayan makonni 32

1.Arsenal-70

2.Manchester City-64

3.Manchester United-55

‘Yan wasa da suka fi jefa kwallaye a raga

1.Erlin Haaland 22 Manchester City

2.Igor Thiago 21Brentford

3.Antoine Semanyo 15 Manchester City

            

La liga:

Juma'a

Real Madrid-Girona 1-1

Asabar

Seville-Atletico Madrid 2-1

Barcelona-Espanyol 4-1

Lahadi

Atletico Bilbao-Villareal 1-2

Jadawalin La liga a mako na 31

1.Barcelona 79

2.Real Madrid 70

3.Villareal 61

‘Yan wasa da suka fi jefa kwallaye a raga

1.Kylian Mbappé 23 Real Madrid

2.Vedat Muriqi 21 Real Mallorca

Serie A:

Juma'a

Roma-Pisa 3-0

Asabar

AC Milan-Udinese 0-3

Atalanta-Juventus 0-1

Lahadi

Parma-Napoli 1-1

Como-Inter Milan 3-4

Jadawalin Serie A bayan makonni 32

1.Inter Milan 75

2.Napoli 66

3.AC Milan 63

‘Yan wasa da suka fi jefa kwallaye a raga

1.Lautaro Martinez 16 Inter Milan

2.Anastasios Douvikas 11 Como

3.Nico Paz 11 Como

Gasar cin kofin zkarun kungiyoyin nahiyar Afirka...

CAF CL zagayen dab da na kusa da na karshe, wasan farko

Asabar

FAR Rabat(Morocco) -RS Berkane(Morocco) 2-0

Lahadi

Esperence(Tunisia) -Mamelodi Sundowns(Afirka ta Kudu) 0-1

Za a buga zagaye na biyu a ranar 18th Afirilu.

CAF Confederation cup zagayen dab da na kusa da na karshe, wasan farko

Juma'a

CR Belouizdad(Algeria)-Zamalek(Egypt) 0-1

Asabar

USM Alger(Algeria)- Olympic Club Safi(Morocco) 0-0

Za a buga zagaye na biyu a ranakun 17th 19th Afirilu.

Yanzu kuma za mu je ga bangaren kwallon tenis...

Tennis:

'Dan wasan Italiya kuma lamba biyu a duniya Jannik Sinner ya koma lamba daya a wannan rana ta Litinin, albarkacin lashe gasar Monte Carlo Masters a birnin Monaco ranar Lahadi, bayan lallasa lamba daya na duniya kuma mai rike da kambun gasar Carlos Alcaraz na Spain.

Wasan wanda ya yi zafi matuka sakamakon jajircewar da zakarun suka yi a yayin fafatawar, lamarin da ya kayatar da 'yan kallo matuka, cikin yanayin kadawar iska mai karfi, inda Sinner ya samu nasara da ci 7-6 (7-5) 6-3.

A bangaren mata kuwa 'yar wasan Rasha Mirra Andreeva ta lashe gasar Linz Open a kasar Austria, bayan doke Anastasia Potapova ta Austria da ci 1-6 6-4 6-3.

Guje-guje da tsalle-tsalle:

A fagen guje-guje da tsalle-tsalle, matashin dan tseren Australia mai shekaru 18 Gout Gout, ya goge tarihin fitaccen zakaran duniya dan kasar Jamica Usain Bolt, bayan da ya lashe tseren mita 200 cikin dakika 19.67, a birnin Sydney ranar Lahadi. A shekarar 2004 mai rike da kambun gasar Olympic har sau takwas Usain Bolt ya samu nasarar lashe gudun mita 200 cikin dakika 19.93, yana da shekaru 17 da haihuwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani