Bitar shekara ta abubuwan da suka faru
December 31, 2015![Nigeria - Präsident Muhammadu Buhari](https://static.dw.com/image/18492902_800.webp)
Talla
Sabon shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sha rantsuwar kamun aiki a ranar 29 ga watan Mayun da ya shuɗe a wani abin da ke zaman ƙoƙari na kafun tarihi na siyasa cikin ƙasar.Dan shekaru 73 Buharin dai yai nasarar karɓe goruba a hannun kuturu a cikin mulki dama siyasar ƙasar dake nuna alamun rikiɗewa ya zuwa tsarin mai ƙarfi sai Allah.