1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blinken na ci gaba da ziyara a Chaina

June 19, 2023

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya isa birnin Beijing na kasar Chaina inda ya fara ziyarar aiki da nufin dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken a birnin Beijing
Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken a birnin BeijingHoto: LEAH MILLIS/REUTERS

Bayan shafe watanni na muhawara da zargin juna, manyan kasashen Amirka da China sun sake tattaunawa kai tsaye da juna a birnin Beijing. Sai dai ra'ayoyin sun bambanta kan ribar da ke tattare da tattaunawar sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da takwaransa na Chaina Qin Gang.

Dama dai dangantaka tsakanin Amirka da China ta kasance a hali mafi muni tun lokacin da aka kulla huldar diflomasiyya, a cewar gidan talabijin na kasar CCTV. A nata bangaren, tawagar ta Amirka ta danganta tattaunawar da wacce ta kasance ''mai amfani kuma cike da gaskiya" bayan taron. Kawo yanzu dai su kansu ministocin na harkokin wajen kasashen biyu ba su ce uffan game da abubuwan da suka tattauna ba.

Amirka da Chaina na takun saka kan batutuwa da dama ciki har da batun tsibirin Taiwan da Beijing ke ikirarin cewar wani yankinta ne, baya ga babutuwa da suka hadar da rikicin kimiya da fasaha, da kuma tursasa wa tsirarun Musulmi na Uighurs da ke Chaina.