Blinken na fifita diflomasiyya a rikicin Nijar
August 15, 2023Wannan shaguben Antony Blinken na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kasashen yammacin Afirka ke kara matsin lamba kan sojojin Nijar don su mayar da mulki ga zababbiyar gwamnati. A lokacin da yake wa manema labarai bayani, Blinken ya nemi da ci gaba da mai da hankali kan hanyoyin sulhu don warware rikicin cikin ruwan sanyi maimakon amfani da mataki na soja.
Shi kuwa firaministan gwamnatin mulkin sojan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine yana ziyarar aiki a kasar Chadi, inda ya gana da shugaban mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno. Sanarwar da fadar mulki ta Ndjamena ta wallafa shafin Facebook ta ce Lamine Zeine ya isar da sako da shugaban hukumar mukkin sojan Nijar ta CNSP ya aika wa takwaransa na Chadi.
A nasu bangaren, shugabannin rundunonin sojojin kasashen yammacin Afirka sun shirya gudanar da taro a birnin Accra na Ghana daga ranar Alhamis, da nufin tattauna yiwuwar kutsawa da makami Nijar domin mayar da shugaba Mohamed Bazoum a kan kujerar mulki. Wannan taron da aka fara dage shi, ya zo ne lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban mulkkin sojan Mali Assimi Goïta suka jaddada mahimmancin warware rikicin na Nijar ta hanyar diflomasiyya.