1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Blinken na ziyara a Koriya ta Kudu

January 5, 2025

Ziyarar ta mista Blinken na da alaka da rikicin siyasa da ya bulla a kasar bayan ayyana dokar soji.

Antony Blinken da Yoon Suk Yeol a ziyarar watan Maris na 2024Antony Blinken da Yoon Suk Yeol a ziyarar watan Maris na 2024Antony Blinken da Yoon Suk Yeol a ziyarar watan Maris na 2024
Antony Blinken da Yoon Suk Yeol a ziyarar watan Maris na 2024Hoto: Evelyn Hockstein/Reuters

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya isa Koriya ta Kudu, a yayin da rikicin siyasar kasar ke ci gaba da rincabewa.

Mista Blinken ya je kasar da ta kasance kawar Amurka ne, bayan tsigaggen shugabanta ya ayyana dokar soja mai cike da cece-kuce a watan Disambar 2024.

An gaza kama shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ke tare da sakataren ya ce, Blinken ya tsara tsayawa a kasashen Faransa da kuma Japan a yayin ziyarar

Wannan balaguron ka iya kasancewa na karshe ga sakataren harkokin wajen na Amurka, ganin cewa an kusa rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaba.

Koriya ta Kudu ta tsige sabon shugaban kasar

Amurka tana da karfin fada a ji a al'amuran Koriya ta Kudu saboda tallafin makamai da jiragen yaki da kuma kyakkyawar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.     

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW