1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Blinken ya tattauna rikicin Gabas ta Tsakiya da Saudiyya

Binta Aliyu Zurmi
October 6, 2024

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken a wata tattauna da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan a kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki.

Saudi-Arabien Riad 2024 | US-Außenminister Blinken trifft Kronprinz Mohammed bin Salman
Hoto: Evelyn Hockstein/AFP/Getty Images

Jami'an diplomasiyyar kasshen biyu sun tattauna batun tabbatar da kudirin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 wanda zai bai wa fararen hula na kasashen Lebanon da Isra'ila koma wa gidajensu.

Kudurin, wanda aka amince da shi a karshen yakin Lebanon na biyu a shekarar 2006, ya bukaci a kawar da wani yanki tsakanin
iyakar Isra'ila da Lebanon har ya zuwa kogin Litani, mai nisan kusan kilomita 30 arewa da kan iyakokin kasashen.

Kungiyar Hizbollah dake samun goyon bayan Iran ta jima tana keta wannan yarjejeniyar a cewar Amurka.

Blinken da bin Farhan sun kuma tattauna bukatar samar da tallafin kasa da kasa ga sojojin Lebanon da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya UNIFIL.

 

Karin bayani:Yaki ka iya mamaye Gabas ta Tsakiya - Scholz