1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobi Wine dan adawa ya fice daga Yuganda

Yusuf Bala Nayaya MNA
September 1, 2018

Mawakin nan da ya rikide zuwa dan siyasa a Yuganda Robert Kyagulanyi ya fice daga kasar don zuwa duba lafiyarsa a Amirka bayan da ya zargi mahukunta a Yuganda da muzguna masa ta hannun jami'an tsaro.

Uganda Kampala Oppositioneller Bobi Wine
Hoto: Getty Images/AFP

Lauyan mawakin ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wannan Asabar. Mawakin na Reggae wanda aka fi sani da suna Bobi Wine ya bata lokaci a ranar Juma'a kafin barin asibitin gwamnati bayan da aka sake tsare shi a lokacin da yake kokarin barin asibiti.

Kyagulanyi ko Bobi Wine dai ya zama dan majalisa a shekarar 2017 inda ya rika jan hankalin matasa, abin da ke zama barazana ga Shugaba Yoweri Museveni. An dai kama shi ne a makon da ya gabata bisa zargin cin amanar kasa bayan da wasu gungun matasa suka jefi motar Shugaba Museveni na Yuganda.