A Yuganda wani makadi da ya rike zuwa dan siyasa, na fatan kawo canji a kasarsa na zama muryar matasa. Bobi Wine wanda ya girma unguwar talakawa, ana masa lakabi da "shugaban unguwar talakawa". Tun bayan shigarsa fagen siyasa, ya zama mai tsananin sukar lamirin shugaban Yuganda Yoweri Museveni.