1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boeing zai samar da manhaja ga jiragensa

Mouhamadou Awal Balarabe
March 28, 2019

Boeing ya bayyana sauye-sauyen da zai yi wa sanfurin jirgin Max 8 don kyautata mu'amala da wadanda ke amfani da su sakamakon faduwar jiragen Habashe da Indonesiya.

USA Renton Boeing 737 MAX geparkt
Hoto: Reuters/L. Wesson

Kanfanin Boeing da ke kera jiragen sama ya bayyana sauye-sauyen da zai yi wa na'urar jirginsa samfurin Max na takwas wanda ya yi hadari a Indonesiya da Habasha a watannin baya. A gaban dimbin manaima labarai a cibiyarsa da ke birnin Renton na Amirka, kanfanin Boeing karkashin shugabanninsa ya ce zai sa wa jirgin wata manhaja da za ta rika gargadi matikar wata matsala ta kunno kai a lokacin tashinsa.

 Boeing ya dauki wannan matakin ne domin kwantar da hankula kanfanonin jiragen sama da ke amfani da sanfurin MAX 8. Amma bai sanar da lokacin da jirgin zi koma bakin aiki ba tun bayan da aka dakatar da amfani da shi a sassa dabam-daban na duniya.

Mutane 346 ne suka rigamu gidan gaskiya a hadura biyu da sanfurin jirgi Max na takwas ya yi a Indonisiya da kuma a Habasha. Sai dai har yanzu masu bincike ba su gano dalilan da suka sa jiragen sanfurin Max na takwas suka rika rikitowa ba.