An gano gawarwaki a gidan kason Chadi
April 20, 2020![Tschad Armee Soldaten Zeremonie](https://static.dw.com/image/19314932_800.webp)
Talla
Mahukuntan kasar Chadi na gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar mayakan na Boko Haram da ake tsare da su a wannan gidan kason, bayan da sojojin Chadin suka fafata da su a yankin Tafkin Chadi. An dai tsare mayakan 58 da nufin gurfanar da su gaban kuliya, inda 44 cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Mahukuntan na Chadi dai sun ce a gwajin da aka yi wa gawarwaki hudu cikin 44 da suka riga mu gidan gaskiya, an gano cewa sun ci guba ne.
Tuni dai masu fashin baki da kuma masu rajin kare hakkin dan Adam, suka bayyana rashin jin dadinsu, ganin cewa ana iya samun bayanai daga bakin wadannan mayakan, inda kuma suka sha alwashin cewa suma za su gudanar da bincike a nasu bangaren, domin gano gaskiyar abin da ya halaka mutanen.