1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin gwagwarmayar ceto 'yan matan Chibok

Uwais Abubakar Idris AMA
April 15, 2019

A Najeriya a daidai lokacin da ake tunawa da ragowar 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram, ra'ayoyi sun banbanta dangane da irin rawa da kungiyar fafutuka ta "Bring Back Our Girls" ta taka wajen ceto 'yan matan

Nigeria Rebecca Samuel Yaga
Hoto: Getty Images/AFP/STRINGER

Da zarar an ambaci ‘yan matan Chibok da Kungiyar Boko Haram ta sace a cikin watan Afrilun 2014 nan take ake tunawa da kungiyar nan ta "Bring Back Our Girls" wadda aka kafa kwanaki 16 da satar 'yan matan. Burinta shi ne fafatukar ganin an maido da 'yan matan da kungiyar ta yi awon gaba da su a gidajensu. Wani matashi ne ya fara da aikawa da sako ta shafin sada zumunta don fargar da jama'a, sannu a hankali sakon ya dauki amo tare da samun karbuwa ga bangarori dabam-dabam na jama'a.

Shugaba Buhari na ganawa da wasu 'yan matan da Boko Haram ta sallamaHoto: Reuters/Presidential Office/B. Omoboriowo

Masana na ganin kungiyar ta yi matukar tasiri wajen cilasta wa gwamnatin Najeriya tattauna wa a karon farko da mayakan kungiyar Boko Haram wanda har ya kai ga samun nasarar karbo wasu daga cikin 'yan matan a hannun kungiyar. Ko da ya ke ra'ayoyin jama'a sun bam-banta game da yadda kungiyar "Bring Back Our Girls" ta karbi mukamai na siyasa daga baya duk da karfin fada ajin da ta ke da shi ga gwamnatin Najeriya.

A yanzu dai sauran matan Chibok 112 da suka ne rage a hannun Boko Haram wadanda suke cika shekaru biyar kenan ba tare da komawa a gidajensu ba. Wannan lamarin ya haifar da fargaba ga iyayen 'yan mata tare da haddasa ragowar zuwa makarantun boko daga ko ina cikin Najeriya musamman ma a arewa maso gabashin kasar da ke fama da tashe-tashen hankula lamarin da yayi tasiri ga harkokin ilimi a Najeriya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani