1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga fargaba a Maiduguri da Damaturu

December 6, 2019

Mazauana kauyukan da ke kan hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri sun shiga rudani bayan da mayakan bangaren Boko Haram wato ISWAP suka yi garkuwa da wasu masu aikin jin kai na Red Cross da kuma wani jami’in Sojoji.

Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

An kame mutanen ne tare da wani jami’in soji da iyalansa da wasu fafaren hula yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri daga Damaturu. Da daren ranar Laraba ne kungiyar ISWAP mai ikirarin kafa Daular Musulunci a yammacin nahiyar Afirka ta yi wa mutanen kwanton bauna ta hanyar kafa shingen bincike a tsakanin kauye Jakana da Mainok da ba su da nisa daga Maiduguri da sunan cewa jami’an tsaro ne ke aikin binciken katin shaidar matafiya.

Kungiyar ISWAP ta ce ita ce ke da alhakin kai harin kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
A cikin irin wannan yanayi ne 'yan kungiyar da ke cikin kayan sarki irin na jami’an tsaron Najeriya suka kamesu tare da tafiya da mutanen 14 a yankunan da suke ke iko da su. Daga cikin wadanda da aka kama akwai Jami’in soji da iyalansa da kuma wasu ma’aikatan agaji da ke aiki da kungiyar Red Cross da kuma wasu fararen hula. A sanarwar da ta fitar na daukar alhakin kame mutanen kungiyar ISWAP ta ce ta kame Sojoji shida da wasu mutane takwas cikin har da ma’aikatan jin kai kuma suna a hannunta tana garkuwa da su. Wannan labari ya saka tsoro a zukatan al’umma musamman matafiya da ke bin hanyar ganin ita ce hanya daya tilo da ake bi ba tare da ba da rakiyar jami’an tsaro ba.
 

Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte