1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa 'yan gudun hijira hari a Kamaru

August 2, 2020

A Kamaru wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun hallaka mutane 13 sun kuma raunata mutum takwas a wani kauye da ake kira Mozogo da ke da iyaka da Najeriya.

Kamerun l Interventionsbrigade "Brigade d'intervention rapide"
Hoto: DW/D. Köpp

Yan ta'addar dai sun jefa gurneti ne a cikin wani dandazon 'yan gudun hijira a harin da suka kaddamar a safiyar Lahadin nan kamar yadda Medjeweh Boukar wani shugaban al'umma a yankin ya tabbatar.

Rikicin Boko Haram da ya addabi yankin tafkin Chadi bai bar Kamaru ba domin a watan Yuni na 2019 mayakan Boko Haram su wurin 300 sun kashe mutane 24 cikinsu har da sojojin Kamaru 16 da ke kan aiki a wani barikin sojoji.