1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta hallaka mutane 7 a Diffa

Abdullahi Tanko Bala
November 23, 2018

Bayan samun zaman lafiya na wani dan lokaci 'yan Boko Haram sun kashe akalla mutane bakwai a wani hari da suka kai kauyen Toumour a jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar.

Niger Flüchtlinge aus Nigeria
Hoto: DW/A. Cascais

A Jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, ma'aikata kimanin bakwai ne na wani kamfanin hakar ma'adanai tare da wani jami'in gwamnati suka rasa rayukansu a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai lokacin da suke barci a gida.

Harin dai ya haifar da fadamuwa a yankin Diffa da ke makwabtaka da tafkin Chadi bayan samun kwanciyar hankali na dan wani lokaci. 

Dukkan mutanen da lamarin ya shafa 'yan Nijar. An kuma harbe su ne a kauyen Toumour da ke iyaka da Najeriya inda suke aikin haka rijiya domin samar da ruwa don inganta rayuwar 'yan gudun hijira da ke zaune a yankin.

Ma'aikatan suna aiki ne da kamfanin Foraco na kasar Faransa wanda ke aikin hakar ma'adanai da kuma rijiyoyin burtsatse.

Wasu mutane biyar sun sami munanan raunuka a kuma garzaya da su asibitin Diffa domin samun magani.

Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da motocin kamfanin guda biyu.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW