Boko Haram ta kai farmaki makarantar 'yan mata
February 20, 2018Talla
Mayakan da suka ja wata tawaga cikin motoci samfurin akori kura ta daukar kaya sun isa kauyen Dapchi a yankin Bursari na jihar Yobe da misalin karfe shida na yammaci inda suka tunkari makarantar kamar yadda Sheriff Aisami wani da ya sheda lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Aisami ya ce da saukar mayakan a garin sun rika harbe-harbe da fasa wasu abubuwa masu kara, wannan ya ja hankalin 'yan makarantar ta 'yan mata da ke garin inda daliban da malamansu suka ranta cikin na kare kafin mayakan su karasa makarantar. 'Yan kungiyar dai ta Boko Haram sun sace kayayyaki da suke bukata a makarantar.