1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kai hari a Kamaru

December 5, 2020

Rahotannin da ke fitowa daga Kamaru, sun tabbatar da wani hari da mayakan Boko Haram suka kai yankin arewa mai nisa mai makwabtaka da Najeriya.

Kampf gegen Boko Haram Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/Ngala Chimtom

Kamar dai yadda bayanai suka tabbatar, harin da aka kaddamar a garin Assighassia, ya yi sanadin mutuwar akalla fararen hula uku da ma jikkatar wasu uku, a cewar Mahamat Chetima Abba, wani basaraken gargajiya a yankin Mozogo.

An dai yi zargin mayakan na Boko Haram sun fitio ne daga Najeriya, suka kuma afka wa mutanen ba-zata.

Wata majiya daga jami'an 'yan sanda da ba ta so a bayyana sunanta ba, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Cikin 'yan watannin nan dai hare-hare daga mayan Boko Haram bangaren Al-Barnawi da ke jagorantar kungiyar ISWAP na kara tsanani a Najeriya da ma kasashe makwabtanta.