Hare hare na ta'azzara a rewacin Najeriya
June 14, 2020Talla
Wani mazaunin garin Munguno ya shaidawa wakilin mu a Maiduguri Al Amin Sulaiman Mohammed cewa, sun yi jana'izar mutane 27 yayin da mazauna kauyen Goni Usmanti suka ce sun gano gawarwaki 37 da mayakan suka hallaka a harin na daren jiya.
Jami'an tsaro sun ce sun dakile harin da mayakan su ka kai a Munguno, sai dai ba su ce komai kan hasarar rayuka da aka samu ba.