1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kauyuka sun fada hannun Boko Haram a Niger

November 16, 2021

Mahukuntan a Najeriya sun sanar da cewa kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta fadada ikonta a kasar. Gwamnatin jihar Neja ta ce kimanin kauyuka shida ne a yanzu ke hannun Boko Haram, a jihar da ke tsakiyar Najeriya.

Nigerianischer Soldat
Hoto: FLORIAN PLAUCHEUR/AFP

A baya dai an fi sanin Boko Haram din a jihohin Arewa maso Gabas, sai kuma ga shi yanzu sun shiga jihar Neja har ma sun fara karbe iko da kayuka.

Sakataren gwamnatin jihar ta Neja Alhaji Ahmed Matane ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA, cewa kauyukan da ke hannun Boko Haram din a Neja na cikin kananan hukumomin Shiroro da Rafi. Jami'in ya ce lamarin ya sanya dubun-dubatar mazauna yankunan kauracewa gidajensu. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW