Boko Haram ta yi wa garin Maiduguri da ke Najeriya kawanya
September 11, 2014Mayakan Boko Haram sun yi kawanya ga garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma suna kokarin yin iko da garin a cewar wasu masu fada a ji daga yankin a ranar Alhamis dinnan. Dattawan sun bukaci a kara adadin yawan dakarun sojan Najeriya da ke a wannan yanki.
Wannan gargadi na manyan tsaffin jami'an gwamnati da tsaffin soji daga wannan yanki, na zuwa ne bayan da Amirka ta yi gargadin cewa ana iya kai hari a wannan birni, a yayin da masana a harkar tsaro ke cewa akwai fargabar gwamnati na iya rasa iko da yankin.
Birnin na Maiduguri na zama wani birni mai muhimmanci ga Kungiyar ta Boko Haram kasancewar wannan kungiya tushen ta ya tsiro ne daga wannan birni a shekarar 2002.
Har ila yau wannan kira na dattawan yankin na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar ta Boko Haram ta kwace wasu kauyuka da garuruwa a jihar ta Borno da Yobe da wasu sassa na jihar Adamawa, duka cikin yankunan da wannan kungiya ke ikirarin cewa nata ne cikin sabuwar daularta ta Islama.