1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Tsugune ba ta kare ba a tafkin Chadi

Al-Amin Suleiman Muhammad June 29, 2015

Kungiyar Boko Haram ce ta fi sauran Kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya yawan kashe jama’a a shekaru biyu da suka gabata, inda Chadi ma ba ta tsira daga hare-hare ba.

Tschad Armee Boko Haram
Dakaru soji da ke tunkarar Boko Haram ta kasaHoto: Reuters/E. Braun

Al'ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya karfafa kokarin da ya ke yi na magance matsalar tsaro da ta addabi shiyar ganin yadda ake samun karuwar hare-haren kunar bakin wake da ake hallaka jama'a.

Shugaban Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren baya bayan nan da aka kai jihohin Borno da Yobe lamarin da ya yi sanadiyar rayuka da dukiyoyin al'umma da dama.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana takaicinsa kan ci gaba da kai irin wadannan hare-hare ya sake jaddada aniyarsa ta murkushe hare-haren kungiyar a daukacin shiyyar da ma Najeriya baki daya.

Neman sauya salo

Wannan Jawabi na shugaban wanda ke zuwa wata guda da kafa gwamnatinsa ya ja hankulan al'ummar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya wanda su ka nemi ya karfafa kokarin da ya ke yi na magance matsalar tsaro da ta addabi shiyyar ganin yadda ake samun karuwar hare-haren kunar bakin wake da ake hallaka jama'a.

Dakarun yaki da Boko Haram na sintiri a ruwaHoto: PATRICK FORT/AFP/Getty Images

Sale Bakuro Sabon Fegi Damaturu na ganin kamata ya yi shugaban ya gaggauta aiwatar da sauye-sauye a dukkanin cibiyoyin tsaro da ake da su, a cewarsa ta haka ne kawai za a iya samun sabbin jini da za su yi aikin tabbatar da tsaron ba kama hannun yaro tunda na yanzun sun kasa.

A cewar Abdulkadir Abab wani da ke bibiyar yadda ake aikin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya ya zama dole shugaban ya samar da wata runduna da za ta hada kai da jama'a don samun saukin wadannan hare-hare.

Kowa na da rawar takawa

Shi kuwa Umar Baba Kumo kira ya yi ga shugaban da ya yi wa sojojin matsin lamba inda kuma ya nunar da cewa aikin ba kawai na jami'an tsaro ba ne dole sai jama'a sun bada tasu gudumowar.

Zaman jiran tsammanin dawowar zaman lafiyaHoto: picture-alliance/dpa/K. Palitza

Yanzu haka dai Kungiyar Boko Haram ita ce ta fi sauran Kungiyoyin ‘yan ta'adda na duniya yawan kashe jama'a a shekaru biyu da suka gabata inda suka kashe sama da mutane dubu 8 kamar yadda wani rahoton wata cibiyar kasar Amurka ta fitar.