1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Lula ya kayar da Bolsonaro

October 31, 2022

Madugun adawar kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi. Sai dai har yanzu shugaba mai ci da ya sha kaye bai ce komai a kan zaben ba.

Wahlen in Brasilien I Ansprache Lula da Silva
Shugaba Lula da Silva da aka sake zaba shugaban BrazilHoto: Carla Carniel/REUTERS

Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya mulki kasar har sau biyu a shekarun baya ya yi kira ga al'ummar Brazil da su kwantar da hankulansu, a daidai lokacin da ake dakon jin martanin shugaba mai ci Jair Bolsonaro wanda ya sha kaye a zaben. A shekara ta 2010 ce dai, Lula da Silva ya mika mulki a matsayin fitaccen shugaba a tarihin kasar. Sai dai daurin watanni 18 a gidan kaso da aka yi masa kan zargin cin hancin da tuntuni aka janye shi, ya zubar masa da mutuncinsa a siyasar kasar. To amma yanzu ana sa ran shugaban mai shekaru 77 a duniya, zai kara gyara kimarsa a yayin mulkinsa karo na uku. A yanzu dai kallo ya koma ga bangaren shugaba mai barin gado Bolsonaro wanda tun kafin bayyana sakamakon, yake zargin an shirya tabka magudi a zaben.