AFCON: Boniface ba zai buga wa Najeria ba
January 9, 2024Duk da cewa ba a yi cikakken bayani ba kan nau'in raunin da ya ke dauke da shi ba, amma dai tuni hukumar kwallon kafar Najeriya ta sanar da Terem Moffi da ke bugawa a Nice na faransa a matsayin wanda zai maye gurbin Boniface.
Tun da farko dai Najeriya da ta lashe kofin sau uku da za ta kara a rukuni daya da Côte d' Ivoire da Guinea-Bissau da Equatorial Guinea, ta raja'a kan Victor Boniface wajen taka rawar gani a gasar ta AFCON.
Idan za a iya tunawa dai, Boniface ya ci kwallaye akalla 10 da hakan ya sa kungiyar ta Leverkusen, kasancewa gagara-gasa a saman teburin gasar Bundesliga a wannan kaka da ake ciki.
Sai dai a wasannin sada zumunci da ta yi, kasar Guinea ta lallasa Nigeria da ci 2-0, da wannan ke kasancewa kalulabe ga Najeriya na lashe kofin Nahiyar Afrika.