Bonn: An yi zanga-zanga kan kare muhalli
November 4, 2017![UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Demonstration & Protest](https://static.dw.com/image/41239334_800.webp)
Talla
Wadanda suka gudanar da zanga-zangar sun hada da masana da kungiyoyi na masu rajin kare muhalli daban-daban. Zanga-zangar na zuwa ne a yayin da ake shirin soma taron kasashen duniya kan sauyin yanayi na duniya wato COP23, taron da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya zai gudana a nan birnin Bonn inda za a kwashe kwanaki 12 ana gudanar da shi. Akalla mutane daga kasashe duniya 196 za su halarci wannan taron da zummar yin nazari kan magance wannan matsalar dumamar yanayi.