Bore a birnin Al-Hoceïma na Maroko
June 28, 2017Talla
Ya zuwa wannan Laraba ba a samu adadin wadanda suka jikkata daga bangaran masu zanga-zangar ba, akasari dai masu zanga-zangar sun yi amfani da duwatsu ne wajen jifan 'yan sandan a cewar hukumomin yankin. 'Yan sandan da suka jikkata sun samun sallama daga asibiti a cewar hukumomin yankin.
An dai gwabza kazamin fada ne tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga tun daga ranar karamar Sallah ta karshen Azumin watan Ramadan a birnin na Al-Hoceïma. Masu zanga-zangar na girgiza acewacin kasar ta Maroko ne tun yau da watanni takwas. A cewar masu zanga-zangar, jami'an tsaron ne suka toshe duk wata kafa tare da hana yin zanga-zanga, abun da ya haifar da dauki ba dadi mai tsananin gaske.