1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da gwamnati a Masar

January 25, 2011

Gwamnatin ƙasar Masar na fiskantar adawa, irin wanda aka yi wa tsohuwar gwamnatin Tunisiya, inda talakawa suka tunɓuke gwamnati.

Wani mai adawa da gwamnatin Masar, ya ke kwatanta yadda ake tsare 'yan adawa a ƙasarHoto: AP

Ɗaruruwan 'yan ƙasar Masar suka shiga wata zanga zangar adawa da gwamnati a birnin Alƙahira. Jam'iyyun adawan ƙasar ne su ka yi ƙira da a ƙaddamar da wannan zanga-zanga irin wanda aka gudanar a ƙasar Tunisiya, domin kawo sauyi na siyasa da na tattalin arziki ga halin talauci da azabtarwa da al'umma ke fama da shi a ƙasar. Wannan dai shine karo na farko da za a gudanar da irin wannan zanga-zanga da ake sa ran za ta tattara jama'a da dama. A 'yan kwanakin baya-bayan nan dai mutane da dama a kasar ta Misira suka bankawa kansu wuta, donmin yin koyi da irin abinda ya faru a ƙasar Tunisiya. Shugaban Hosni Moubarak wanda ke da shekaru 82 da haifuwa, ya kwashe kusan shekaru 30 ya na yin mulki, kuma har yanzu yana shirin ko dai ya yi ta zarce ko kuma ya ɗora ɗansa ya gaje shi.

Mawallafi: Harouna Mamman Baƙo

Edita: Usman Shehu Usman.