1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da matakan tsimi a Sudan

September 27, 2013

Tun wasu kwanaki kenan dubban 'yan Sudan a fadin kasar ke zanga-zangar nuna adawa da matakan tsimin kudi da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir ke aiwatarwa.

Sudanese anti-government protesters chant slogans after the Friday noon prayer in the Omdurman district of northern Khartoum, Sudan, Friday, Sept. 27, 2013. Security forces opened fire on Sudanese protesters Friday, witnesses said, as thousands marched through the streets of the capital in an opposition push to turn a wave of popular anger over fuel price hikes into an outright uprising against the 24-year rule of President Omar al-Bashir. (AP Photo/Khalil Hamra)
Hoto: picture alliance/AP Photo

Tashoshin telebijin na kasashen Larabawa sun ce muatne kimanin 30 aka kashe, amma masu fafatuka na ikirarin cewa a Khartoum kadai, mutane 100 aka kashe.

Bakin hayaki ya tirnike sararin samaniyar Khartoum babban birnin kasar Sudan, wuta na ci a gidajen mai sannan masu zanga-zanga na yi ta kona tayoyin mota don nesanta kansu daga dakarun tsaro. 'Yan adawa da shugaban Sudan Omar al-Bashir suna wannan bore na gama gari don adawa da matakin tsimi da shugaban ya sanar a ranar Lahadi da ta gabata.

"Abubuwa uku suka jawo matsalolin tattalin arzikinmu. Na farko sh ne kayan da muke shigowa da su sun fi wanda muke fitarwa yawa, muna amfani da kayan da ya fi wanda muke samarwa, sannan ma'aikatar kudi na kashe kudi fiye da wanda take samu. Da yawa na cewa janye tallafin man fetir zai fi shafar talakawa. Amma ka da sun manta cewa ci gaban matsalar tattalin arziki zai kara wa talaka wani nauyi."

Shugaban Sudan Omar al-BashirHoto: Ashraf Shazly/AFP/Getty Images

Adawa da matakin tsuke bakin aljihu

Sai dai matakin tsimin bai samu karbuwa ba domin tun wasu kwanaki da suka gabata dubban 'yan kasar ke yi ta zanga-zanga adawa da matakin ninka farashin man fetir har sau biyu da tsadar sufuri abin da ya yi tasiri ga farashin kayan abinci. Kungiyoyin adawa na zargin cewa shugaba al-Bashir na bukatar karin kudi domin yakar 'yan adawa kamar yadda Amgad Farid mai fafatukar girke mulkin demokradiyya ya nunar.

"Dukkan al'ummar Sudan ta ki wannan mataki na danniya. Gwamnati na kashe kudi domin muzguna wa 'yan adawa da kuma sayen makaman yakin da take yi. Mai ya sa ba za ta iya samar wa al'ummarta abinci da kuma man fetir ba?

Shi kuwa Bashir Adam Rahma na jam'iyyar adawa ta Popular Congress cewa ya yi.

"Gwamnati na fama da matsaloli domin kasafin kudinta ya rushe. Saboda haka take neman kudi da za ta kashe wa gwamnati da kuma jam'iyyar Congress ta shugaba Bashir. Tana bukatar karin kudi ga yakin da take yi a lardin Darfur da Kordofan ta Kudu da kuma yankin Blue Nile."

Barazana ga gwamnatin al-Bashir

An yi ta kone-kone a lokacin borenHoto: Reuters

Shin kowace irin bazarana wannan bore ke da ita ga karfin ikon shugaba al-Bashir. Florian Dähne shi ne wakilin gidauniyar Jamus ta Friedrich Ebert dake birnin Khartoum ya ce ko shakka babu boren wata bazarana ce ga gwamnatin Sudan.

"Ko da yake kawo yanzu zanga-zangar ba ta kai karfin da za ta kai ga kifar da gwamanti nan gaba kadan ba, amma wata damuwa ce ga gwamnati dake fama da matsalolin tattalin arziki da na siyasa wanda zai iya ta'azzara sakamakon wannan bore."

Tun dai fara boren a farkon wannan mako mutane da yawa sun rasa rayukansu. Sai dai masu fafatuka na kara kira ga jama'a su ba su goyon baya a kokarinsu na neman 'yancin walwala, zaman lafiya da kuma adalci a kasar ta Sudan.

Mawallafa: Hans-Michael Ehl / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh