1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da tsare 'yan jarida a Turkiya

December 29, 2016

A daidai lokacin da wasu 'yan jaridar Turkiya ke bayyana a gaban kotu bayan cafkesu a watan Augusta, wasu masu gangami a birnin Istanbul sun yi tir da tauye 'yancin fadan albarkacin baki a kasar.

Türkei Protest gegen Verfolgung von Journalisten der Zeitung Özgür Gündem
Hoto: picture-alliance/L. Pitarakis

 

Masu gangami sun yi cincirindo a kofar wata kotu da ke birnin Istambul a safiyar Alhamis, domin nuna goyon bayansu ga ma'aikatan kamfanin wata jarida da ake zargi da goyon bayan 'yan tawaye kurdawan Turkiya. An fara shari'ar Asli Erdogan da Necmiye Alpay da wasu marubuta a kasa, a wani mataki da masana ke bayyanawa da kokarin toshe bakin 'yan jaridar kasar. Labarin kama dan jarida Ahmet Sik ya kara harzuka masu gangamin adawan.

Baris Yarkadas mamba ne na hukumar lura da 'yan jarida na jam'iyyar adawa CHP ya ce " A yayin da muka zo nan domin ganin shari'ar Asli Erdogan da Alpay, da sauran 'yan jarida, wadanda abokanmu ne, mun samu labarin cewar 'yan sanda sun kama wani dan jarida kuma abokinmumai suna Sik, saboda wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter. Ana ci gaba da cin zarafin 'yan jarida . Bayan kasancewa a tsare na kwanaki 132, a karon farko abokanmu zasu gurfana a gaban alkali".

Shari'ar na zuwa ne a daidai lokacin da aka cafke Ahmed Sik, a binciken da ake yi a kan wani labari da ya yayata ta shafinsa na twitter da jaridar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya nunar.Tun a watan Augusta ne dai aka cafke marubucin littattafai Asli Erdogan da marubuci a kan harsuna Necmiye Alpay  tare da wasu mutane 8 da ke aiki a kamfanin wata jarida mai suna Ozgur Gundem da ke goyon bayan kurdawa.   

Hoto: picture-alliance/abaca/Depo Photos

Masu shigar da kara a Turkiya na muradin kotu ta zartar da daurin shekaru masu yawa na zaman wakafi a kan 'yan jaridar saboda kasancewarsu masu goyon bayan kungiyar tawaye ta PKK, batu da a cewarsu ke barazana ga hadin kan Turkiya tare da yayata farfaganda na ayyukan ta'addanci.

Hukumomin Turkiyyar sun jima da farautar 'yan jaridar kasar, kamar yadda shugaban kungiyar 'yan jarida na kasar Gokhan Durmus ya nunar..Ya ce" 'Yancin tofa albarkacin baki da walwalar 'yan jarida na cikin mawuyacin hali a Turkiya. A yanzu haka akwai 'yan jarida sama da 100 da ke kurkuku. Muna bukatar gwamnati ta sakesu. Muna muradin ganin kotu ta wanke wadannan 'yan uwa namu da aka gurfanar a gaban kotu".

Kwamitin kula da 'yan jarida mai matsuguni a birnin  New York na kasar Amurka ta shaidar da cewar, akalla 'yan jarida 81 ke garkame a kurkukun Turkiya, daura da rufe kafofin yada labaru sama da 130. Tun bayan rusa shirin kifar da gwamnatin kasar a watan Juli. Ana zargin 'yan jarida da marubuta da laifukan yayata farfaganda na ayyukan ta'addanci.