1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren Hong Kong ya shiga mako na 22

Abdul-raheem Hassan
November 2, 2019

A karon farko masu zanga-zangar neman 'yancin Hong Kong daga gwamnatin Beijin sun dira a kan wani ofishin dillancin labaran China da ke yankin domin nuna fushinsu.

China Hongkong l Proteste - "Notruf" für Autonomie
Hoto: Shannon Stapleton/REUTERS

Masu aiko da rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun farfasa gilasan ofishin tare da shafa jan fenti a jikin ginin sannan suka cinnawa ofishin wuta. 'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da fesa ruwa mai karfi don tarwatsa dandazon masu boren.

Wannan dai shi ne mako na 22 da 'yan fafitikar yankin Hong Kong ke jerin zanga a cikin watanni biyar, da zimmar samun cinkakken 'yancin cin gashin kai daga gwamnatin China.