1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren kin jinin gwamnati ya karu a Sudan

Binta Aliyu Zurmi MAB
February 28, 2023

Daruruwan 'yan Sudan sun sake fantsama a kan titunan birnin Khartum don nuna adawa da ci gaba da rike madafun iko da gwamnatin rikon kwarya ta soji ke yi.

Masu zanga-zanga na kalubalantar jami'an tsaro a SudanHoto: AFP/Getty Images

A zanga-zangar ta wannan Talata, an yi fito na fito tsakanin masu boren da jami'an kwantar da tarzoma na Sudan, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare ma da harba albarusai da harsasan roba.  Daya daga masu boren ya riga mu gidan gaskiya bayan da harsashi ya ratsa kirjinshi.

Kasar ta Sudan ta shiga cikin halin rashin tabbas tun bayan da sojoji suka hambarar da halartaciyar gwamnatin farar hula. A karshen shekarar da ta gabata ne, shugabannin soji da na farar hula suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rigingimun da suka mamaye Sudan tun bayan kifar da mulkin kasar.