1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren masu rajin kare muhalli a Turkiya

June 1, 2013

Zanga-zangar da aka fara a birnin Santanbul na Turkiya ta bazu zuwa wasu manyan biranen kasar, inda ta rikide zuwa wani boren kin jinin gwamnati.

Riot police use tear gas to disperse the crowd during an anti-government protest at Taksim Square in central Istanbul June 1, 2013. Turkish police fired tear gas and water cannon for a second day on Saturday to prevent hundreds of protesters reaching the central Taksim Square, scene of violent protests in which hundreds were injured on Friday. REUTERS/Murad Sezer (TURKEY - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

'Yan sandan kasar Turkiya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi, kan masu zanga-zanga a birnin Santanbul, abin da ya janyo jikata mutane masu yawa, kuma yanzu haka wannan zanga-zanga ta bazu zuwa wasu biranen kasar da suka hada da Ankara babban birnin kasar da garin Izmir mai tashar jiragen ruwa. Zanga-zangar ta Santanbul ta samo asali ne, saboda nuna adawa da sare bishiyoyi 600 a wurin shakatawa na birnin, domin gina manyan shaguna. Tuni ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta Turkiya, ta ce za ta binciki zargin amfani fiye da karfi da 'yan sanda suka yi. Kamar yadda 'yan sanda suka nunar an kame mutane fiye da 60 wadanda suka shiga zanga-zangar ta neman kare wurin shakatawa na Gezi-Parks inda ake shirin wani gagarumin aikin gine-gine. A wasu wuraren zanga-zangar ta rikide zuwa boren kin jinin manufofin gwamnatin Firaministan Recep Tayyip Erdogan mai ra'ayin mazan jiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal