Boren neman sauyi a Saudiyya
December 28, 2012Yan sandan Saudi Arabiya sun bindige mutun guda har lahira a boren neman sauyi dake gudana a gabashin kasar. Mutumin da ya mutu a yau, shine cikamako mutane 12 wadanda jami'an tsaron Saudiya suka hallaka tun fara boren neman kifar da gwamnati, a dai-dai lokacin da ake zanga zanga a sauran kasashen Larabawa domin kawar da shugabannin kama karya. A kasar Saudiyya dai an fi gudanar da zanga-zanagar neman sauyi ne a gabashin kasar, inda yan Shi'a suka fi yawa, kana kuma jahar ta Qatif itace ta fi arzikin man fetur. Masu boren dai suna bore ne domin neman a sako dimbin yan fafitika wadanda jami'an tsaron Saudiyya suka kame, inda yan sanda suka bude wuta suka hallaka Ali Al-Marar ,dan sheakru 18 da haifuwa, kana suka raunata a kalla mutane shida. Kakakin yan sandan jahar yace yan sandan na kokarin kwantar da tarzumar da ake yi ne, inda mutane suka rufe hanya da tayoyin mota. A kasar Saudiyya dai ana yin boren neman sauyi tun sama da shekaru biyu, to amma ba da safai batun ke fitowa a kafa yada labaran duniya ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamad Awal Balarabe