1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240311 Syrien

March 27, 2011

Gwamnatin Siriya ta ɗage dokar ta ɓaci wanda aka yi shekaru fiye da arba'in ana amfani da ita, abinda ke nuna bada kai ga masu boren neman sauyi.

Masu adawa da gwamnatin Siriya ke boreHoto: picture alliance/abaca

Sannun a hankalin dai guguwar neman sauyi dake kaɗawar a ƙasashen Larabawa, yanzu ta mamaye ƙasar Siriya, ƙasar da ita ce mafi gaba da Isra'ila kuma mafi ɗasawa da ƙasar Iran, idan aka kwatanta ta da sauran ƙasashen Larabawa. Don haka shakka babu wannan tarzuma a ƙasar Siriya tana da tasiri ga ƙasar Isra'ila.

Gwamnatin ƙasar Siriya kamar sauran ƙasashen Larabawan da masu nemnan walwalar demokraɗiyya suka yi bore, da fari jami'an tsaron ta sun fara tarwaza duk wata zanga zanga. To amma boren wanda ya faro daga birnin Dera'a dake lardin Hauran wanda ke kan iyakarsu da ƙasar Jodan, yanzu ya yaɗu izuwa sassan ƙasar. Kawo yanzu ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty international tace an halaka a ƙalla mutane 50, a karawar da jami'an tsario ke yi da masu boren. Sannu a hankali yanzu boren neman sauyin ƙasashen larabawa ya kasance wani ƙalubale ga shugaba Bashar Al'Assad, inji wani shehin malamin Islama Udo Steinbach.

"Wannan guguwar sai ƙara fantsama take yi, daga wannan ƙasar Larabawa izuwa wancan. Kuma wannan ƙasar Siriya ba za ta zira ba. Gwamnatin Damaskus ba za ta kasance ta bambanta da sauran ba"

Sojojin gwamnatin SiriyaHoto: AP

Siriya ta bambanta da sauran Larabawa

Shima Andre Bank na cibiyar natsarin harkokin Gabas ta Tsakiya dake birnin Hamburg, yace gwamnatin Al-Assad na cikin mawuyacin hali matsi, kuma kujerar Bashar Assad ta na rawa. Wani abinda ke ɗan taimakawa shugaban dai shine aksarin jami'an gwamnatin sa matasa ne ke tafiyar da mulki. Kuma tabbas a ƙasar Siriya akwai bambanci tsakanin tsafin kurayen shugabannin da suka fice a cin hanci, a ra'ayin masanin Gabas ta Tsakiya Andre Bank.

"Idan har wannan tarzuma kan shugaba Bashar ta kasance kamar wanda ta kifar da gwamnatin Mubarak da Ben Ali da shugaba Saleh na Yaman. To mutun zai iya cewa matasan ƙasar Siriya ba su fahimci tarihin ƙasarsu ba"

Wani abinda ya bambanta ƙasar Siriya da sauran ƙasashen Larabawa da ake neman sauyi shine, duk da cewa mabiya sunni suka fi rinjaye a ƙasar dama a gwamnati, to amma fa suma ma biya Shi'a marasa rinjaye suna cikin jam'iyya Ba'ath mai mulkin ƙasar kana 'yan shi'an suna cikin masu faɗa aji na jami'an leƙen asirin ƙasar.

Shugaban ƙasar Siriya Bashar El AssadHoto: picture-alliance/ dpa

Shin ko sojoji za su juwa shugaban baya

"Saɓanin abinda ya faru a ƙasar Masar inda sojoji suka juyawa Mubarak baya, a ƙasar Siriya soji da jami'an leƙen asiri basa su juyawa Bashar baya ba. sabo da sun san cewa idan gwamnatin Assad ta zo ƙarshe to suma tasu ta zo ƙarshe kenan"

Bashar Al-Assad wanda ya karanci ilimin likitan idanu a birnin London, a shekara ta 2000 ya karɓi mulki bayan da mahaifinsa Hafiz Al-Assad ya rasu. Da farko ya fiskanci matsalolin kawo sauyi daga jam'iyarsa ta Ba'ath da kuma jami'an tsaron ƙasar. To amma masana na cewa har yanzu tattalin arzkin ƙasar yana cikin koma baya, ga kuma rashin aikin yi ga matsa.

Mawallafa Domink Peter da Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi