Boren soji a kasar Guinea Bissau---
October 7, 2004Rahotanin dake fitowa daga kasar Guinea Bissau a yau alhamis,sun yi nuni da cewar sojin kasar da suka kashe shugaban sojin kasar sun gabatar da jerin wasu bukatu da suke so a biya musu da suka hadar da gagauta biyan su albashin da suke bin gwamnati,sai kuma kara musu yawan albashi da kyautata zaman su a barikokin su.
Tun a jiya laraba ne dai sojin kasar Guinea Bissau suka gudanar da bore,wanda a cikinsa suka kashe baban hafsan sojin kasar Ganar Verissimo Sebra da kuma mai magana da yawun hukumar soji Laftanar kanal Domingos Barros,kamar yadda wanan sanarwar ta fito daga jami’an gwamnatin ta kasar Guinea Bissau.
Yau alhamis ne dai ake sa ran sojin dake bore a kasar ta Guinea Bissau zasu zauna kann teburin sulhu da jami’an gwamnatin farar hula na wanan kasa ta yammacin Africa da nufin kawo karshen boren da sojin kasar suka shiga na neman a biya musu bukatun su.
An dai shafe kusan sa’oi bakwai ana tattauna yadda za’a sami masalaha ta sulhu da sojin dake bore a kasar ta Guinea Bissau amman kuma wanan taro ya kare ba tare da cimmma biyan bukata ba.
A halin yanzu dai an fara samun kwanciyar hankali a Bissau fadar mulkin kasar Guinea Bissau,tun da shike a yau alhamis an sami sukunin bude ofisoshin gwamnati da makarantu kamar yadda aka saba,babu kuma sojoji masu yawa a kann titunan birnin na Bissau.
Gidan Radion din kasar Portugal na RDP dake yadda shirye shiryensa ga kasahen Africa ya bada labarin cewar sojin dake bore a kasar Guinea Bissau sun bada wata sanarawa inda suka bukaci a kara musu yawan albashi,kuma a kawo karshen matsaloli na karbar rashawa a hukumar sojin kasar.
Bugu da kari wasu rahotanin kuma na cewar sojin dake bore a kasar Guinea Bissa,sun dauki mataki na kashe manyan jami’an sojin kasar ne a matsayin ramuwar gaya kann jami’an sojin da suke adawa da su tun bayan wani yunkurin juyin mulki da soji suka yi shekarar data gabata a kasar ta Guinea Bissau.
Sanawar data fito daga ministan tsaron kasar Guinea Bissau Daniel Gomes ta baiyana cewar sojin da suka yi wanan bore basu jima da dawowa daga aiyuka na kiyaye zaman lafiya a Liberia ba karkashen majalisar dikin duniya,kuma sun dauki wanan mataki ne don nuna fushin su kann rashin biyan su albashin su a kann kari.
A yanzu haka dai kungiyar kasahe bakwai dake magana da harshen Portugues sun aika ministan harkokin wajen kasar East Timor zuwa kasar Guinea Bissau a matsayin mai shiga tsakani,don tabatar da ganin an kawo karshen boren da soji ke yi a kasar Guinea Bissau.
Haka zalika ana sa ran Mohammed Ibn Chambas sakataren kungiyar habaka tattalin arzikin kasahen Africa ta yamma,zasu tashi zuwa kasar ta Guinea Bissau shida ministan harkokin wajen kasar Senegal a matsayin masu shiga tsakani.
Kasar dai ta Guinea Bissau mai yawan aluma 1.3 ta sha fama da matsaloli boren soji,tun lokacin da aka fara gudanar da mulki na democradiya a kasar a shekara ta 1994.