1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren sojoji a Burkina Faso

April 18, 2011

Boren jami'an tsaron Burkina Faso ya kama manyan biranen ƙasar guda huɗu

Shugaba Blaise CompaoreHoto: picture-alliance/ dpa

Mazauna garin Kaya a Burkina Faso, sun ce sojoji da 'yan sandan garin sun tayar da tarzoma tun daga daren jiya, bayan da suka afkawa titunan ƙasar suna harbe-harbe a iska, domin nuna adawar su da shugaban ƙasa Blaise Compaore

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya rawaito cewa, jami'an tsaron, sun ƙona gidan shugaban na su, kana suka kuma bincike gidan wani babban hafsan sojin ƙasar.

Zanga-zangar ya yi mafari ne a makon jiya, daga Wagadugu babban birnin ƙasar wanda aka sanya wa dokar ta ɓaci tun ranar alhamis ɗin da ya gabata, kuma ya bazu zuwa manyan garuruwan Po da Tenkodogo

A yunƙurin ciyo kan rikicin, Compaore ya rusa gwamnatin sa a ran juma'ar da ta gabata ya kuma zaɓi sabbin hafsoshin Soji kuma gwamnatin ta sa ta ce za ta hukunta duk jami'an tsaron da ke nuna bijirewa.

Tashe-tashen hankulan dai ya kai ga jikkatar mutane kimanin 45 wadanda a yanzu haka ke kwance a asibiti.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal