Boren 'yan Masar a ofishin jakadancin Isra'ila
September 10, 2011Jakadan Isra'ila a Masar ya fice daga birnin Alkahira da asubahin wannan rana ta asabar bayan da masu zanga-zanga suka afka wa ofishin jakadancin Israilan tare da lalata wani ɓangare na ginin. Tuni dai gwamnatin riƙon ƙwaryar Masar ta kira wani zaman majalisar ministoci na gaggawa domin nazarin hanyoyin da za a ɓullo ma wannan batu.
Ɗaruruwan 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma sojoji sun jikata masu boren da dama, a lokacin da suka tarwatsa gangamin yin Allah wadai da kashe jami'an tsaron Masar biyar da isra'ila ta yi a kwanakin baya. Masu zanga-zangar sun ƙona tutar isra'ila tare da yin kaca-kaca da shinge da aka kafa tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen biyu domin kare ofishin jakadancin Isra'ila da ke masar.
Tun bayan hamɓarar da gwamnatin kama karya ta Hosni Mubarak a watan Fabrairu, wasu 'yan Masar suka fara kiraye kirayen katse yarjejniyar zaman lafiya da ƙasarsu ta cimma da Isra'ila shekaru 31 da suka gabata.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala