1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: Ganawar Johnson da Macron

August 22, 2019

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya gana da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, a ci gaba da neman daidatawa da kungiyar Tarayyar Turai game da sassauta matsayi kan abin da ya shafi kan iyakar Jamhuriyar Ireland.

Frankreich Emmanuel Macron und Boris Johnson in Paris
Hoto: Reuters/G. Fuentes

Batun cimma matsaya kan makomar iyakar Jamhuriyar Ireland din dai, na zaman karfen kafa game da ficewar Birtaniya daga EU. A ranar Larabar da ta gabata, Mr. Boris Johnson, ya gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan batun, musamman don Birtaniya ta iya ficewa cikin girma da arziki.


Shugaban Macron din da ke karbar bakuncin Firaministan na Birtaniya, daya ne daga cikin wadanda ke da tsanani game da ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. Kungiyar dai ta sha nanata cewar babu abin da zai saka ta sauya daga abin da kasashen suka cimma da Birtaniya cikin watan Mayun da ya gabata dangane da duk wani abin da ya shafi amincewar ta fice daga cikinsu.To sai dai a yayin ganawar da ya yi da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda kusa ce a kungiyar gamayyar kasashen Turai, ta ce tana iya yiwuwa a cimma matsaya game da yankin nan mai sarkakiya na iyakar Jamhuriyar Ireland wanda ke a cikin Tarayyar Turan kafin cikar wa’adi na ranar 31 ga watan Oktoba.

Boris Johnson ya gana da Angela Merkel kan ficewar Britaniya daga Kungiyar EUHoto: Reuters/F. Bensch

Shi kuwa Firaministan Birtaniya Boris Johnson, wanda ya yi ziyararsa ta farko a Jamus bayan zama jagoran gwamnati, ya yi marhabin ne da labarin da ya ji daga Angela Merkel. Amma kuma ga alamu, ya amince cewar shawara ta rage wa kasarsa ta iya samar da masalaha ta yanda za ta iya ficewa da yarjejeniya, saboda bayanan da ya yi na abin da za su yi kan iyakar Jamhuriyar Ireland da ke zama babbar tarnakin arziki ga Birtaniyar muddin ta fice ba tare da yarjejeniyar ba.

A na shi bangaren, Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, aza ayar tambaya ya yi a kan ko da gaske Firaministan na Birtaniya Boris Johnson ke yi, ko kuma dai kokari ne na dora wa kungiyar EU laifi, idan aka ki amince masa da bukatar. Batun iyaka tsakanin Jamhuriyar Ireland da ke cikin Tarayyar Turai da kuma Ireland ta Arewa da ke cikin Birtaniya dai, yarjejeniya ce da tsohuwar Firaministar Birtaniya Theresa May ta amince da kungiyar a baya, sai dai sau uku majalisar dokokin Birtaniyar na fatali da shi.

Shugaban sashin harkokin noma na Tarayyar Turai, ya yi gargadin cewa idan har Birtaniyar ta fice daga EU ba tare da cimma matsaya a ranar 31 ga watan Oktoba ba, to hadari ne da ka iya shafar duk wani batu na kasuwanci da sauran kasashe 27 mambobin kungiyar da kuma Birtaniyar.