1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Coronavirus: Boris Johnson ya killace kansa

Abdourahamane Hassane
March 27, 2020

Firaminista Birtaniya ya kamu da cutar Coronavirus kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwar fadar gwamnatin.

Großbritannien London | Coronavirus | Boris Johnson, Premierminister
Hoto: picture-alliance/empics


Boris Johnson ya ce ya fara jin zazzabi kana yana tari ya ce bisa umarnin likitocinsa ya yi gwajin cutar Coronavirus kuma aka ce ya kamu da ita. Boris din ya ce ya killace kansa amma dai yana ci gaba da jagorantar harkokin gudanarwa na mulki. Sannan maidakinsa wacce ke da juna biyu an wareta daga gidan na iyali kamar yadda gwamnatin ta bayar da umarni.