1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Karuwar wadanda suka kamu

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 27, 2020

Wata sanarawar fadar gwamnatin Birtaniya, ta bayyana cewa Firaminista Boris Johnson ya kamu da cutar Coronavirus, inda a yanzu haka ya killace kansa.

Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris JohnsonHoto: picture-alliance

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce zai ci gaba da jan ragamar mulki, duk da ya kamu da cutar Coronavirus. Johnson dai ya ce ya fara jin zazzabi ne kana yana tari, inda bisa umarnin likitocinsa ya yi gwajin cutar Coronavirus kuma aka ce ya kamu da ita. Boris din ya ce ya killace kansa amma dai yana ci gaba da jagorantar harkokin gudanarwa na mulki. Sannan maidakinsa wacce ke da juna biyu an wareta daga gidan na iyali kamar yadda gwamnatin ta bayar da umarni.

Sabuwar tungar Coronavirus

Amirka dai ta kasance sabuwar tungar Coronavirus a duniya, bayan da ta zarta kowacce kasa a yawan wadanda suka kamu da cutar ta Coronavirus. Yayin da adadin wadanda suka mutu a kasashen Italiya da Spain da a nahiyar Turai, ya zarta adadin wadanda suka mutu a kasar Chaina inda cutar ta samo asali. Yayin da Jamus ta kasance kasar da ke da karancin wadanda suka mutu sakamakon annobar ta Coronavirus cikin manyan kasashen duniya.


A Najeriya kuwa, kamfanoni da attajiran cikin kasar ne suka sanar da wani sabon tsarin da zai  samar da daukacin kudaden da ake da bukata domin yakar annobar da ke ta yaduwa. Kama daga gwamnatin da ta tsaida aiyyuka da kuma masu kasuwa da ke kirga asara dai, Tarayyar Najeriyar tana ganin daban sakamakon annobar. To sai dai kuma 'yan kasuwar kasar sun kai ga yunkuri da nufin cike gibi na kudaden da gwamnatin kasar ke da bukata domin wannan yaki.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote a Najeriya Aliko DangoteHoto: picture-alliance/dpa/C. Petit Tesson

Tallafi daga kamfanoni da attajirai

A wajen wani taro da babban bankin kasar na CBN ya jagoranta dai, wasu manyan kamfanoni na kasar kusan 20 sun yanke shawarar bayar da tallafin da bai gaza  Naira Miliyan Dubu daya ba kowannensu da nufin gina cibiyoyin killace kai da kuma samar da kayyayakin gwaji da kare kai da ake da bukata. Dangote Foundation da hadin gwiwar bankin Access dai alal ga misali, sun yi alkawarin gina wata cibiyar killace al'umma mai gado dubu ko bayan kayan gwajin da za a raba a biranen kasar daban-daban.

Akalla Naira Miliyan Dubu 120 ne dai Tarayyar Najeriyar ta ce tana da bukata da nufin tunkarar annobar, cikin kasar da ke fuskantar radadi na faduwar farashin man fetur. Ya zuwa ranar yau dai mutane 65 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya, yayin da aka sallami guda uku mutum guda kuma ya rigamu gidan gaskiya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani