1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Sabon hari a garin Rann

January 15, 2019

Mayakan Boko Haram sun kai wani hari a garin Rann shalkwatar karamar hukumar Kalabalge da ke jihar Borno a Tarayyar Najeriya, inda su ka tarwatsa dubban 'yan gudun hijira.

Nigeria Maiduguri Zerstörte Häuser nach Boko Haram Attacke
Boko Haram sun kona gidaje a RannHoto: Getty Images/AFP/A. Marte


Mayakan na Boko Haram sun afkawa garin Rann ne a daidai lokacin da ake yin sallar Magariba inda su ka bude wuta kan jami'an tsaro da sauran mutanen gari. Bayanai da ke fitowa daga wasu mazauna garin wanda su ka tsere zuwa wasu kauyuka da ke kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Kamaru, sun tabbatar da cewa mayakan sun ci karfin jami'an tsaro, innda suka janye suka koma Gamboru-Ngala. Wannan ya sa al'umma da yawancin 'yan gudun hijira suka tsere, abin da ya bai wa mayakan Boko Haram din damar kona gidaje da Tantuna na 'yan gudun hijira gami da wasu ofisoshi na gamnati da cibiyoyin kula da lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma motocin da ke lodin kayan abinci da manyan dakunan ajiye abincin da ake tallafawa 'yan gudun hijira.

Babu dai cikkaken bayani kan yawan wadanda harin ya rutsa da su, sai dai ana fargabar an samu asarar rayuka da kuma jikkata, kana babu masaniya kan halin da darururuwan 'yan gudun hijira da ke da samun mafaka a garin na Rann wadanda yawanci suka gudu cikin jeji domin tsira da rayukansu ba. Ana dai ci gaba da nuna damuwa kan sababbin hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai wa, inda yawanci ake alakanta dagulewar lamarin da siyasa kasancewar zabe na gabatowa. Yanzu haka dai akwai al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kamar malam Adamu Dan Borno da ke cewa ba su ga nasarar da ake cewa an  samu a yakin da ake yi da kungiyar ta Boko Haram ba. Bayanai da ke fitowa daga garin na Rann na nunar da cewa mayakan na Boko Haram sun fice bayan da jami'an tsaro suka koma tare da tallafin sojojin da ke Gamborun-Ngala da kuma jiragen yaki da su ka musu rakiya. Sai dai babu wani bayani daga wajen hukumomi ko jami'an tsaro kan wannan hari ya zuwa lokacin hada wannan rahoto. 

Boko Haram sun tarwatsa 'yan gudun hijira a sansaninsu da ke RannHoto: Silas Adamou/Ärzte ohne Grenzen