1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwararar 'yan gudun hijirar Damasak zuwa Diffa

April 15, 2021

Hare-haren Boko Haram sun tilastawa daruruwan mazauna garin Damasak na jihar Borno tserewa zuwa jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.

Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

A yankin Jahar Diffa da ke gabashin Jamhuriyar Nijar sabbin 'yan gudun hijira daga Damasak ne ke ci gaba da kwarara zuwa yankunan kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro. Hakikan ci gaba da samun wasu sabbin 'yan gudun hijirarda yankin na Diffa ke yi, ya biyo bayan harin da mayakan  Boko Haram bangaren ISWAP suka kai garin Damasak da ke a shiyyar arewa maso Gabashin tarayyar Najeriya a daf da karshen makon da ya gabata.

Karin Bayani:  ISWAP ce ta kai wa sojojin Nijar hari

'Yan gudun hijirar Diffa da matsalar tsaro ta raba da gidajensuHoto: Getty Images/AFP/O. Omirin

Daga Gaggam da ke karamar hukumar Shetimari zuwa garuruwan bakin kwalta, tun daga jihar Diffa har zuwa Maine Soroa, rohotanni na cewa 'yan gudun hijira ne suka tare, wani malami da ya bukaci a sakaye sunansa, ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yo hijira a ranar Laraba daga Damasak zuwa Gaggam. A yanzu dai bayan matsugunni da kuma dan abin buda baki da suke samu, makomar ilimin yaran da aka nemi mafaka da su na daga cikin abubuwan da 'yan hijirar ke kokawa a kai. Wannan dai, ba shi bane karon farko da garin Damasak ke fuskantar munmunar harin mayakan na Boko Haram, da ke tilasta musu tserewa daga kasar suna neman mafaka a jamhuriyyar Nijar.

Karin Bayani:  Ruɗani a kan batun sace mata da yara a Damasak

'Yan gudun hijira na fuskantar karancin abinciHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A dai ranar Larabar da ta gabata ne, a Najeriyan, mayakan Boko Haram suka sake kai wani sabon hari a garin na Damasak da ke zama cibiyar karamar hukumar Mobar a Jihar Bornotare da karbe ikon garin. Ana dai fargabar mutane da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata. Yanzu haka dai akwai dubban mutane da suka makale a daji ba su samu isa yankunan da su ke son zuwa ba. Ana fargabar da dama sun shiga mawuyacin hali da ma kamuwa da cututtuka kuma babu ma’aikatan jin kai da za su taimaka musu. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani