ICC ta samu Bosco Ntaganda da laifi
July 8, 2019Kotun da ke zamanta a birnin The Hague na kasar Neatherlands, ta ce ta samu Ntaganda mai shekaru 45 a duniya da laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa a yayin yakin basasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a tsakanin shekarun 2002 zuwa 2003 a yankin arewacin kasar. Gaba daya alkalai uku masu yanke hukunci sun amince da samun Ntaganda da daukacin tuhumar da aka yi masa kan laifuka guda 18, inda 13 suka kasance laifukan yaki kana biyar ke zaman na cin zarafin dan Adam, sai dai sun ce za a jinkirta har sai an tantance irin hukuncin da ya dace da shi. A shekara ta 2013 ne dai Ntaganda da ya kasance babban jami'in harkokin soja na kungiyar 'yan tawayen UPC daga shekara ta 2002 zuwa 2005 ya mika kansa ga kotun, sai dai ya musanta baki dayan zarge-zargen da ake masa da suka hadar da gana azaba ga mutane da kisan kare dangi na kabilanci da kuma fyade ga mata gami da saka yara aikin soja, laifukan kuma da kotun ta ICC ta ce ta same shi da aikatawa baki daya, wanda kuma ka iya sanyawa ya fuskanci hukuncin daurin rai da rai.