Bouteflika: Ba zan kammala wa'adi ba
March 4, 2019Talla
Shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Aljeriya, ya yi alkawarin cewar ba zai kammala wa'adin da yake nema na shugabancin kasa ba, idan har aka sake ba shi damar mulki a zaben watan gobe na Afrilu da za a yi a kasar.
Shugaban dai na wadannan kalamai ne, yayin da zanga-zanga ke kara zafi daga masu adawa da ci gaba da mulki da yake yi da a yanzu ya doshi shekaru 20.
A shekara ta 2013 ne dai Shugaba Bouteflika, ya kamu da cutar shayewar wani sashe na jiki.
Daruruwan dalibai ma dai sun yi dafifi a Algiers da wasu manyan biranen kasar a jiya, duk a adawa da mulkin shugaban mai shekaru 82. 'Yan sanda sun yi ta fesa ruwan zafi kan masu boren, a kokarin hana su isa muhimman wurare a birnin na Algiers.